kasar Rasha ta musanta amfani da jirage marassa matuka na kasar Iran a yakinta da kasar Ukraine
Kasar Rasha ta yi watsi da zargin amfani da jirage marassa matuki na kasar Iran a yakin ta da kasar Ukraine, tana mai cewa Rasha ta gwammace yin amfani da jirage marasa matuka a cikin gida. Da aka tambaye shi a Yau Talata ko Rasha ta yi amfani da jiragen Iran marasa matuki ko kuma ta siya, kakakin fadar shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov ya ce na’urorin da ake amfani da su a yakin kasar Rasha ne. “A’a, ba mu da irin wannan bayanin. Kayan aikin da ake amfani da shi na kasar Rasha ne. Kun san haka. Yana da sunayen Rashanci. Kuna iya amsa duk wasu tambayoyi ga ma'aikatar tsaro," in ji shi. Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi ikirarin cewa an yi amfani da jiragen Iran marasa matuki a harin da aka kai a safiyar ranar Litinin a Kiev babban birnin kasar Ukraine. A lokuta da dama Iran ta yi watsi da rahoton "marasa tushe" game da aika jiragen yaki marasa matuka zuwa Rasha da za a yi amfani da su a yakin kasar...