Rundunar Yan sandan jihar Jigawa ta yi nasarar cafke wasu manyan yan bindiga Masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa




 Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayyana haka ta bakin mai magana da yawun rundunar, Lawan Shisu Adam, a hedikwatarsu da ke Garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa.





 Lawan Shisu ya tabbatar da cewa sun samu bayanan sirri game da mutane, dalilin hakan shi ne sun hada kai da wasu jami’ai masu bawa  jami’an tsaro Hadin kai  domin kama su.




 Majiyar Jaridar Arewa ta ruwaito cewa rundunar ‘yan sandan ta gudanar da aikin ne a wasu kananan hukumomin jihar Jigawa Da Jahar kano.






 Mutanen biyu da aka kama da laifin garkuwa da mutane, sun hada da Safiyanu Muhammad mai shekaru 35, wanda ke zaune a garin Arababa da  ta Gabas a jihar Kano.




 Sai kuma Musa Idi, dan shekara 40, haifaffen Gurgunya, karamar hukumar Taura, Jihar Jigawa.




 Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, Shisu Adamu ya kara da cewa sun gano AK 47 guda 1, AK 2, da layukan waya.




 Haka kuma  Lawan Shisu Adam ya ce akwai zargin kashe jami’in shige da fice a lokacin da yake aiki a kusa da kauyen Kilbu na karamar hukumar Binniwa, a ranar 9/8/2022, kuma ana zargin mutanen da aka Kama da kisan.




 Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa Bashir Ahmad ya ce da zaran sun kammala bincike za su gurfanar da su a gaban kotu.

Comments