shugaban kasar Iran Ibrahim Raeisi ya sha alwashin cewa Iran za ta bi diddigin kisan gillar da aka yi wa babban kwamandan yaki da Kungiyoyin Ta'addanci Na Duniya na kasar Iran Janar Qassem Soleimani
Shugaba Raeisi ya bayyana hakan ne ga kungiyar Majalisar dinkin duniya a birnin New York, inda ya kai ziyara.
Shugaban Kasar iran ya yaba da rawar da Iran ta taka wajen fuskantar manyan tsare-tsare da manufofin shiga tsakani, gami da "ta'addancin da Amurka ta kirkiro."
Ya yi nuni da, godiya ga kwamandan Marigayi Janar Qsim Soleimani, kasar Iran ta yi nasarar dakile makircin da aka kulla da nufin karkatar da madafun iko na kasashen yankin.
"Za mu bi diddigin gurfanar da tsohon shugaban Amirka [Donald Trump] a kotu ta hanyar adalci," in ji Raeisi.
Comments